Connect with us

News

Hisbah ta kama wanda ake zargi da bokanci a Kano

Published

on

Hisbah ta kama wanda ake zargi da bokanci a Kano

Hukumar Hisbah ta jahar Kano, ta kama Wani mutum Mai suna, Umar Sokoto, Dan Shekaru 50, bisa zarginsa da harkar Bokanci da kuma yada Badala shida Wani matashi Wanda suke harkar Kawalci.

Hukumar ta cafke mutanen ne biyo bayan korafe-korafen da al’ummar Sheka layin Chairman , a karamar hukumar Kumbotso,suka Yi kan Zargin Bokanci da Kawalcin da Ake Yi a yankin.

Advertisement

Jami’an sun Bayyana cewa, an samu mace da namiji a gidan mutumin, Wanda yanzu haka Ake ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.

Haka zalika an samu wasu kayayyaki , a gidan da Ake Zargin ana yin amfani da su.

Advertisement

Sai dai mutanen sun musanta Zargin bokanci, Amma sunce hada mata da Maza waje guda ba daidai ba ne kuma ba za su kara ba.

Umar Sokoto ya ce baya yin Bokanci Amma Yana bayar da maganin Neman farin Jini ga mata , kuma yau shekarun sa biyar Bai taba Samun matsala da kowa ba, Inda yanzu haka ya ce zai koma gida Sokoto bayan an Yi masa wa’azi kuma ya daina.

Advertisement
READ ALSO  Ex-Real Madrid player discovers through DNA test that his baby isn't his after getting a tattoo

Copyright © 2024 Davida Communications. All rights reserved.