Connect with us

News

Kwankwaso ba zai koma APC ba – NNPP

Published

on

Kwankwaso ba zai koma APC ba – NNPP

Shugaban Jam’iyyar NNPP reshen jihar Kano, Hashimu Suleiman Dungurawa, ya karyata jita-jitan cewa shugaban jam’iyyar na ƙasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, zai koma jam’iyyar APC, yana mai cewa wannan zargi ne kawai don bata sunansa.

Dungurawa ya gargadi Shugaba Bola Tinubu da ya shirya shan kasa idan ya yanke shawarar yin takara a wa’adi na biyu a zaben 2027.

“Da waɗannan tsauraran manufofin ka na ƙuncin rayuwa ga talakawa, kawai ka shirya fuskantar faduwa a zaɓe mai zuwa. Ko ka canza tsare-tsarenka, ko kuma mu ‘yan Najeriya tare za mu canza ka,” in ji Dungurawa a ranar Alhamis.

Yayin da yake nuna tabbacin cewa NNPP za ta samu nasara a duk jihohin Najeriya 36 da kuma zaɓen shugaban ƙasa a 2027, ya ce ‘yan Najeriya yanzu sun gane, suna goyon bayan NNPP.

Dungurawa, wanda ya yi magana da manema labarai a Kano, ya ƙara da cewa:
“Daga ranar 29 ga Mayu, 2023, Shugaba Tinubu ya fara bayyana manufofin da ke cutar da talakawa, kuma kamar dai mun yi masa laifi, ya ci gaba lafta mana irin wadannan manufofi.”

Ya bayyana cewa jam’iyyarsa ta buɗe ofisoshi kuma ta kafa tsare-tsare a jihohi da kananan hukumomi a faɗin ƙasar, yana mai cewa wannan ci gaban alama ce a fili cewa NNPP za ta lashe kujerun jiha da na tarayya a 2027.

A cewarsa, NNPP ta samu nasarori masu yawa a 2024, kuma tana kan hanyar cim ma ƙari a 2025.

Dungurawa ya jaddada cewa ƙalubalen da jam’iyyar ke fuskanta kawai shi ne zargin cewa Gwamnatin Tarayya tana da shirin maida ƙasar tsarin jam’iyya ɗaya.

Ya shawarci Gwamnatin Tarayya da ta ƙara ƙoƙari wajen kawo manufofin da za su rage wahalhalun da mutane ke fuskanta.

Copyright © 2024 Davida Communications. All rights reserved.